Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: Wasu yan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Magu, sun kashe jami’in dan sanda

Yanzu Yanzu: Wasu yan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Magu, sun kashe jami’in dan sanda

A daren jiya wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai hari gidan mukaddashin shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rasahawa (EFCC), Mista Ibrahim Magu sun kuma kashe wani jami’in dan sanda.

A cewar bincike, yan bindigan sun kai farmaki gidan gonan a Karshi dake babban birnin tarayya da misalign karfe 10 na daren ranar Talata sannan sukayi musayar wuta da jami’an yan sandan dake gadi.

An bigi wani Sajan na yan sanda sannan ya mutu a take.

Yanzu Yanzu: Wasu yan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Magu, sun kashe jami’in dan sanda

Yanzu Yanzu: Wasu yan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Magu, sun kashe jami’in dan sanda

Wannan shine karo na biyu day an bindiga ke kai hari gidan.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya yabawa Sanatocin Arewa

Watanni 10 da suka shige ya kasance kalubale ga Magu saboda yaki dukar da kai ga matsin lambar da wasu manyan yan siyasa suka sa masa.

Bayan barazana da ake ta Magu da iyalansa hakan yasa aka zuba jami’an yan sanda a gidansa dake Karshi wanda ba’a kammala ba.

Haka zalika wasu sun kai farmaki gidan iyalinsa dake babban birnin jihar Borno sannan sunyi barazana ga matar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel