Nigerian news All categories All tags
'Yan fansho sun tsayar da Gwamna Tambuwal takara a zaben 2019

'Yan fansho sun tsayar da Gwamna Tambuwal takara a zaben 2019

Da alama dai duniya tayi dadi bayan da hadaddiyar kungiyar 'yan Fansho ta kasa reshen jihar Sokoto watau Nigerian Union of Pensioners (NUP) a turance suka bayyana aniyar su ta sake tsaida Gwamnan jihar takarar Gwamna a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar ne dai ta Nigerian Union of Pensioners (NUP) watau Alhaji Ummaru Abubakar ya sanar da shawarar da suka yanke ga manema labarai a jihar yayin da suke bukukuwan zagayowar ranar 'yan fanshon ta duniya.

'Yan fansho sun tsayar da Gwamna Tambuwa takara a zaben 2019

'Yan fansho sun tsayar da Gwamna Tambuwa takara a zaben 2019

KU KARANTA: Saudiyya ta halasta gidajen Sinima a kasar

Legit.ng dai ta samu cewa Alhaji Umaru ya kara da cewa sun yanke wannan shawarar biyo bayan tattaunawa da suka yi a tsakanin su suka kuma jinjinawa Gwamnan wajen yadda ya biya su dukkan hakkokan su da suke bin gwamnatin a jihar.

Daga nan ne ma dai sai shugaban kungiyar ta Nigerian Union of Pensioners (NUP) ya bayyana cewa tuni kungiyar ta su ta sha alwashin zata saiwa Gwamnan fom din sake takarar a dukkan jam'iyyar da ya zaba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel