Yaki da rashawa: Tsohon gwamnan jihar Kebbi zai bayyana a gaban Kotu

Yaki da rashawa: Tsohon gwamnan jihar Kebbi zai bayyana a gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Sa’idu Nasamu Dakingari zai gurnafana gaban kuliya manta sabo sakamakon tuhume tuhumen badakalar karkatar da kudaden al’umma da hukumar ICPC ke yi masa.

Shugaban hukumar yaki rashawa da dangoginta mai zaman kan ta, ICPC na jihar Sakkwato, Bulus Mai ne ya bayyana haka a ranar bikin yaki da rashawa na Duniya, a jihar Sakkawato.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Kotu ta watsa ma Saraki kasa a idanu a shariar sa da kotun da’ar ma’aikata

Daily Trust ta ruwaito Bulus yana fadin cewar a satin nan ne hukumar zata tasa keyar Dakingari, tare da tsohon sakataren gwamnatin jihar, in da ya kara da cewa hukumar na bukatar hadin gwiwar jama’a wajen yakar da rashawa yadda ya kamata.

Yaki da rashawa: Tsohon gwamnan jihar Kebbi zai bayyana a gaban Kotu

Hukumar ICPC

Majiyar Legit.ng ta jiyo Bulus yana shaida ma daliban kwalejin tarayya ta Sakkwato cewa suna da muhimmin rawa da zasu taka game da yaki da rashawa, musamman a irin wannan rana.

Shugaban yace dalibai ka iya shirya zanga zangar lumana don goyon bayan yaki da rashawa, haka zalika suna iya wayar da kan jama’a a shafukan sadarwa na zamani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel