Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin PDP na kokarin ganin Kwankwaso ya fice daga APC

Gwamnonin PDP na kokarin ganin Kwankwaso ya fice daga APC

- Gwamnonin PDP sun fitar da ‘Yan takarar su a zabe mai zuwa

- Daga cikin jerin babu wani ‘Dan kudu sai Gwamnan Jihar Ribas

- Haka kuma babu sunan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku

Yanzu haka maganar da ake yi Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun fitar da ‘Yan takarar Shugaban kasa a zaben 2019 kuma babu sunan Atiku Abubakar. Inji Jaridar The Nation. Da alama Atiku dai ya dawo PDP ne saboda ya tsaya takara a 2019.

Gwamnonin PDP na kokarin ganin Kwankwaso ya fice daga APC

Atiku zai fuskanci sabuwar matsala a Jam’iyyar PDP

‘Yan takarar da Gwamnonin PDP su ka fitar su ne: Tsohon Gwamnan Jihar Kano da Jigawa watau Malam Ibrahim Shekarau da kuma Sule Lamido. Sannan Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo da wasu da ke cikin Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Makarfi yayi magana karo na farko bayan sauka daga Shugaban PDP

PDP na sa rai tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso ya dawo Jam’iyyar da ya bari a da. Sannan kuma Gwamnonin PDP na kokarin ganin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar.

Watau dai babu sunan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar duk da cewa yana da goyon bayan tsofaffin Shugaban Kasar nan amma Gwamnonin da su ka daura Uche Secondus a matsayin Shugaban Jam’iyyar ba ta shi su ke yi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel