Nigerian news All categories All tags
Babu son rai wajen zaben PDP da aka yi Inji Makarfi

Babu son rai wajen zaben PDP da aka yi Inji Makarfi

- Tsohon Shugaban na P.D.P ya bayyana abin da ya kawowa Yarbawa cikas

- Ahmad Makarfi yace Yarbawa sun kasa fitar da ‘dan takara guda a zaben

- Makarfi yace bayan haka kuma wasu daga Yankin sun koma zagin Jama’a

Sanata Ahmad Muhammad Makarfi yayi magana karo na farko bayan ya sauka daga matsayin na Shugaban Jam’iyyar adawa na PDP na Kasa a karshen wannan makon. Makarfi kuma yace an yi gaskiya wajen zaben.

Abin da ya hana Yarbawa kawo sabon Shugaban PDP Inji Makarfi

Tsohon Shugaban PDP Sanata Ahmad Muhammad Makarfi

Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana abin da ya kawowa Yarbawa cikas a wajen zaben Shugabannin Jam’iyyar da aka yi a Ranar Asabar wanda yace Mutanen Kudu maso Yamman sun gaza fitar da wani tsayayyen ‘Dan takara a zaben inda Uche Secondus yayi nasara.

KU KARANTA: Zaben PDP ya bar baya da kura bayan da Yarbawa su kayi bore

Yace da farko an fitar da ‘Dan takara guda daga Yankin sai kuma kawai wani yaje yace shi fa bai janye ba don kuwa har yanzu yana cikin masu nema a wajen zaben. Wannan abu ya kawo rikici ana shirin zaben. Yarbawa dai sun yi tir da wannan zabe da aka yi.

Ahmad Makarfi ya kuma ce wasu mutane daga Yankin sun rika suka da kuma zagin ‘Yan Jam’iyyar ta PDP babu gaira babu dalili. Tsohon Shugaban na PDP yace wannan yana cikin abin da ya kawo cikas amma yace babu wani coge da aka yi zaben ko kadan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel