Sabon Shugaban Rundunar Soji da ke Borno ya sha alwashin ganin karshen Boko Haram

Sabon Shugaban Rundunar Soji da ke Borno ya sha alwashin ganin karshen Boko Haram

- Sabon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya ya gargadi Boko Haram

- Manjo Janar Rogers Nicholas yace zai kawo karshen ‘Yan ta’addan

- Janar din yace Sojojin Najeriya na shirin hada kai da Jama’an Kasa

Labari ya kai gare mu cewa Sabon Shugagaban Rundunar Sojojin Najeriya da aka aika Yankin Borno ya sha alwashin ganin karshen ‘Yan ta’addan Boko Haram cikin dan kankanin lokaci.

Sabon Shugaban Rundunar Soji da ke Borno ya sha alwashin ganin karshen Boko Haram

Sabon Shugaban Rundunar da ke filin daga a Borno

Sabon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya da ke bakin daga a Maiduguri watau Manjo Janar Nicholas Rodgers ya gargadi ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka rage da su ajiye makamin su domin neman sulhu tun da sauki a Kasar.

KU KARANTA: Boko Haram: Sojojin saman Najeriya sun aika Runduna Kasar waje

Janar Nicholas ya bayyana wannan ne a a farkon makon nan yayin da da yake wata ganawa da ‘yan jarida. Janar din yace za a kawo hanyoyi domin ganin karshen ‘Yan ta’ddan na Boko Haram da su ka koma iya dasa bam su tsere.

Nicholas ya nemi hadin kan Jama’ar Yankin wajen yaki da ‘yan ta’ddan. A karshe Janar Nicholas din yace Sojojin Najeriya na shirin hada kai da ‘Yan Jaridu a Kasar domin kawo karshen ta’addancin na Boko Haram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel