Nigerian news All categories All tags
Kaduna: An cafke wadanda ake zargi da garkuwa da hadimin sanata Sani

Kaduna: An cafke wadanda ake zargi da garkuwa da hadimin sanata Sani

- Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da kame daya daga cikin wadanda suka sace hadimin sanata Shehu Sani

- Wasu 'yan bindiga da ba’a sani ba sun yi garkuwa da Mallam Bashir Ahmed a Kaduna

- Sanata Shehu Sani ya ce mutumin da aka yi garkuwa da shi mataimakinsa ne a kan harkokin matasa

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da kame mutumin da ake zargi da hannu wajen sace wani mataimaki ga sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai.

Wasu 'yan bindiga da ba’a sani ba suka yi garkuwa da hadimin sanatan a Kaduna.

Mazauna sun ce mataimakin, Bashir Ahmed, kuma malami ne a wata makarantar Islama mai zaman kansa a Tudunwada, Kaduna.

Kaduna: An cafke wanda ake zargin da garkuwa da hadimin sanata

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai

Shaidun da suka yi magana da majiyar Legit.ng sun ce, 'yan bindigar sun yi wa Mista Ahmed wulakanci kafin su yi awon gab da shi a cikin wata motar Hilux Van.

KU KARANTA: Nasir El-Rufai da matarsa sunyi shar a sabbin hotuna

"’Yan bindigar sun zo tare da bindigogi, sun rufe fuskokin su, sun yiwa Mallam Bashir Ahmed dukan tsiya kafin su tafi da shi a cikin Hilux Van. Kowa a wannan lokacin na kokarin kare kansa. Wannan lamarin mai ban tsoro ne", in ji Abdul Mansur.

Mukhtar Aliyu, mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda a jihar Kaduna, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, ya ce "an kama daya daga cikin wadanda suka sace Mallam Ahmed, kuma bincike yana ci gaba".

Mista Aliyu ya kara da cewa hukumar ta yi zargin cewa akwai makirci a lamari, kuma wadanda suka aikata laifin ba su tambayi wani fansa ba har yanzu.

Mista Sani, wanda ya tabbatar da labarin ga wakilinmu, ya ce mutumin da aka yi garkuwa da shi mataimakinsa ne a kan harkokin matasa, kuma 'yan bindiga sun sace shi a Tudunwada Kasuwan Barci a karfe 9 na dare a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel