Nigerian news All categories All tags
Kasar China ta hana mutanen ta shiga Kasar Israila saboda danyen aikin Trump

Kasar China ta hana mutanen ta shiga Kasar Israila saboda danyen aikin Trump

– Shugaba Trump ya ayyana Kudus a matsayin babban Birnin Israila

– Wannan abu ya sa Kasar China ta haramtawa mutanen ta zuwa Israila

– Kasar Jafan ma dai ta dakatar da ziyarar da ta shirya zuwa Kasar a da

Mun ji cewa nanyan Kasashen Duniya irin su Kasar China da Jafan sun taso Shugaban Kasar Amurka Mista Donald Trump a gaba game da matakin da ya dauka na maida Garin Kudus a matsayin babban Birnin Kasar Israila kwanan nan.

Kasar China ta hana mutanen ta shiga Kasar Israila saboda danyen aikin Trump

An tasoTrump a gaba bayan maida Kudus Hedikwatar Israila

A makonnin nan ne Shugaban na Amurka Trump ya ayyana Garin Kudus a matsayin babban Birnin Kasar Jersulem wanda hakan ya tada zauna tsaye a Duniya. Kasashen Jafan da China sun dakatar da shirin ziyartar kasar Israila kamar yadda su ka shirya.

KU KARANTA: Sabon matakin da Donald Trump ya dauka ya fara kawo rikici

Kamar yadda rahoto ya zo mana daga gidan yada labarai na TRT, Kasar Jafan ta ce tana fatan wannan mataki da Shugaba Trump ya dauka ba zai kawo cikas a wajen harkar kasuwancin ta da Kasar Israila ba kamar yadda aka saba.

Bayan nan kuma Kasar Sin watau China ta haramtawa mutanen Kasar ta ziyartar Israila saboda wannan mataki da Amurka ta dauka bayan da Trump ya dauke hedikwatar Israila daga Birnin Tel Aviv zuwa Garin Kudus kwanaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel