Kungiyar nakasassu ta koka cewa ba’a damawa da su a gwamnati

Kungiyar nakasassu ta koka cewa ba’a damawa da su a gwamnati

- Kungiyar nakasassu reshen jihar Cross Ribas ta koka cewa ba’a damawa da su a gwamnati

- Kungiyar ta zargi gwamna Ayade cewa ya ki sake musu kudin yayin bikin ranar nakasassu na duniya ta shekarar 2017

- Okon ya roki gwamna Ayade cewa ya cika alkawurran da ya yiwa nakasassu a jihar

Kungiyar nakasassu wtau Living with Disabilities (PLwDS), reshen jihar Cross Ribas sun yi zargin cewa gwamna Ben Ayade na jihar ya manta da su.

Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar ta yi zargin cewa gwamna Ayade ya ki sake musu kudin gudanar da ayyuka yayin da suke bikin zagayowar ranar nakasassu na duniya ta shekarar 2017 wanda ake yi a ranar 3 ga Disamba na kowace shekara.

"Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Ribas ya yi watsi da nakasasu a jiharsa", in ji kungiyar a cikin wata sanarwa da Comrade Offiong Okon ya sanya.

Kungiyar nakasasu ta koka cewa ba’a damawa da su a gwamnati

Comrade Offiong Okon

"Maimakon haka, ya yi amfani da kudaden a matsayin cin hanci ga ‘yan majalisar dokokin jihar don su ba shi damar gabatar da kasafin kudi na naira tiriliyan 1.3”.

KU KARANTA: Yara dubu 170 ke hawa yanar gizo a kullum - UNICEF ta yi gargadi

"Ya ƙi amince da dokar nakasasu bayan amincewar majalisar dokoki akan dokar, ya kuma ƙi yin gyara game da aikin Comrade Ogar Inyang a matsayin mataimaki na musamman ga gwamna (SA) a kan harkokin nakasassu”.

Okon ya roki gwamna Ayade cewa ya cika alkawurran da ya yiwa nakasassu a baya don domin a dama dasu a gwamnati.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel