Kotun daukaka kara ta haramtawa hukumar EFCC binciken alkalai

Kotun daukaka kara ta haramtawa hukumar EFCC binciken alkalai

-Kotun koli tace EFCC bata da hurumin binciken alkalai

-Alkalai da yawa na fuskantar tuhumar cin hanci daga hukumar EFCC

-Wannan hukunci ya soke hukuncin da wata kotu ta yi tun a farko

Wata babbar kotun Najeriya dake zaman ta a jihar Legas tace hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) bata da hurumin gurfanar da alkalai bisa tuhumar su da cin hanci, matukar suna matsayin su na alkalai ba tare da hukumar kula da ma’aikatar shari’a ta sallame su daga bakin aiki ba.

Kotun koli ta haramtawa hukumar EFCC binciken alkalai

Kotun koli ta haramtawa hukumar EFCC binciken alkalai

Alkalin kotun, Hydiazira Nganjiwa, ne ya yanke wannan hukunci a yau yayin sauraron tuhumar da hukumar EFCC ke yiwa wasu alkakalan kasar nan.

DUBA WANNAN: Babban Bankin kasa zai haramtawa masu taurin bashi samun rance daga Bankuna

Wannan hukunci na kotun ya share hukuncin farko da wata kotun a jihar Legas ta yanke.

Hukumar EFCC na binciken alkalai da dama bisa zargin su da karbar na goro domin dakile adalci.

Da yawan ‘yan Najeriya na dora laifin tafiyar wahainiya da shari’ar masu cin hanci ke yi, da karbar na goro da alkalai ke yi, domin abu ne mai matukar wuya ka ji kotun Najeriya ta yanke hukunci mai tsanani ga shugabannin da aka samu da hannu dumu-dumu wajen sama da fadi da dukiyar al’ummar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel