Nigerian news All categories All tags
Masu garkuwa da mutane sun ci karensu ba babbaka a jihar Neja a jiya

Masu garkuwa da mutane sun ci karensu ba babbaka a jihar Neja a jiya

Masu garkuwa da mutane na ci gaba da cin karensu babu babbaka, inda ko a jiya Lahadi 10 ga watan Disamba, sai da barayin suka yi awon gaba da mutane goma, tare da kashi guda uku.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa garin Sarkin Pawa, dake cikin karamar hukumar Munya, na jihar Neja, kamar yadda jarida Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Abin kunya: Jami’in hukumar kare hadɗura ya gwada ƙwanji da wata mata a kan titi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan al’ummar yankin, Sanata David Umoru ne ya bayyana haka, inda yace jama’ansa ne suka sanar da shi faruwar, Sanatan ya kara da cewa ragora barayin mutane da jami’an tsaro suka tarwatsa su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ne suka koma jihar Neja.

Masu garkuwa da mutane sun ci karensu ba babbaka a jihar Neja a jiya

Masu garkuwa da mutane

A cewar Sanata, akalla kauyuka goma sha biyar ne barayin suka kai ma farmaki. Dayake bayani a kan faruwar lamarin, kwamishinan Yansandan jihar Dibal Yaradi yace tun daga 5 ga watan Disamba zuwa 10 ga watan Disamba, barayi sun sace mutane tara a garin munya da Shiroro.

“An saci mata uku a kauyen Janja, inda aka kashe mahaifinsa, sa’annan ana saci mata uku a Shoho Kibla duk a cikin karamar hukumar Munya, inda aka saci wasu mata uku a kauyen Erena dake Shiroro.”

Duk dayake ba’a san inda matan Munya suke ba, amma an kama barayin da suka sace matan garin Erena, bayan sun sako daya daga cikin matan, tare da bata lambar waya da za’a kira su, inji kwamishinan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel