Nigerian news All categories All tags
Abuja: Dokpesi ya yi amai ya lashe, ya taya Secondus murna

Abuja: Dokpesi ya yi amai ya lashe, ya taya Secondus murna

- Cif Raymond Dokpesi ya taya sabon shugaban jam’iyyar PDP murnar lashe zabe

- Dokpesi ya bayyana cewa wakilai na PDP sunyi magana ta hanyar zabe

- Tsohon dan takarar shugabancin PDP ya ce Allah ya albarkaci jam'iyyar PDP

Cif Raymond Dokpesi, jigo kuma wanda ya yi takarar shugaban jam'iyyar PDP kuma ya rasa, ya taya Yarima Uche Secondus murnar lashe zaben.

Dokpesi, wanda ya yi watsi da yadda aka gudanar da taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba ya bayyana cewa "wakilai sunyi magana".

"Ina godiya ga wakilai akan zaben da suka yi a wannan taron da kuma taya murna sabbin shuwagabanin jam'iyyar da aka zaba a karkashin jagorancin Secondus.

Abuja: Dokpesi ya yi amai ya lashe, ya taya Secondus murna

Cif Raymond Dokpesi

"Za ku iya tuna cewa na ce duk abin da ya faru a wannan zaben, cin gaban PDP ita ce na farko”.

KU KARANTA: Abuja: Yadda PDP ta raba shugabanin jam’iyyar a sabbin mukamanta

"Allah ya albarkaci jam'iyyar PDP. Na taya jam’iyyar murna da kuma dukkanin mambobinmu baki daya", in ji Dokpesi.

A halin yanzu, sabon shugaban PDP, Yarima Uche Secondus, ya yi alkawarin cewa jam'iyyar a karkashin jagorancinsa, za ta ci gaba da bin tsarin mulkin dimokradiyya ta cikin gida da manufar da za ta mayar da hankali ga 'yanci.

Idan dai baku manta ba Legit.ng ruwaito cewa Cif Raymond Dokpesi da Farfesa Tunde Adeniran, sun ki amince da sakamakon zaben jam'iyyar, yayin da Dokpesi ya yi zargin tafka magudi a tsarin zaben.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel