Nigerian news All categories All tags
Lema ta yage a taron PDP na shiyyar yankin Arewa Maso Yamma, Namadi Sambo ya fice a fusace

Lema ta yage a taron PDP na shiyyar yankin Arewa Maso Yamma, Namadi Sambo ya fice a fusace

- Masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso yamma sun tashi baram-baram a taron da suka gudanar a tsakinin su a ranar Juma'a

- Manyan yan PDP reshen Arewa maso yamma sun bukaci a samu matsaya guda wajen tsayar da yan takara a mukaman da aka ba shiyyar fitar

- Rashin jituwa ya sa Namadi Sambo ya fice a fusaci kafin su kammala taron

Legit.ng ta samu rahoton yadda rikici ya barke tsakanin jigajigan jam'iyyar PDP shiyyar Arewa maso Yamma a ranar jajibarin babban taron da jam’iyyar PDP na kasa ta gudanar a ranar Asabar.

Rikicin ya barke ne bisa zargin yukurin nuna karfa-karfa wajen dora yan takara a wasu mukamai.

Masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso yamma sun tashi baram-baram a taron da suka gudanara a gidan tsohon jakadan Najeriya Aminu Wali dake Abuja har ta kai da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya fice daga taron a fusace.

Lema ta yage a taron PDP na shiyyar yankin Arewa Maso Yamma, Namadi Sambo ya fice a fusace

Lema ta yage a taron PDP na shiyyar yankin Arewa Maso Yamma, Namadi Sambo ya fice a fusace

Manyan yan jam’iyyar PDP shiyyar yankin Arewa maso yamma, sun bukaci a samu matsaya guda wajen tsayar da yan takara a mukaman da aka ba shiyyar ta fitar, ba sai an kai da yin zabe ba.

KU KARANTA : Babu abin da ke sosa mani rai kamar in ga yara sun fito gani na – Inji Buhari

An ba yanki Arewa maso yamma damar fitar da sakatren jam’iyya na kasa, mataimakin ma’ajai na kasa, da mai ba da shawara akan al’amurarran sharia.

Sai wani mai suna Mashi yace hakan ba zai yiwu ba saboda kowain da takara ya kashe kudi ya saya dan bin kudirin sa kuma an tanatance shi, don haka a bar dimokradiyya ta yi aikin ta.

Mashi ya ce ba a tuntubi su ba tuntuni game da wannan kudiri sai da yanzu da aski ya kai gaban goshi.

Daganan aka fara ceckuce har ta janyo tsohon mataimakin shugaban kasa Namdi Sambo ya fice a fusace kafin sun kamala taron.

A cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekaru, tsohon gwamnan Kaduna Ramalan Yaro, tsohuwar minitsar kudi Nenadi Usman, Senata Danjuma La’ah, da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel