Tsadar mai: Gwamnatin tarayya tayi karin haske game da karin kudin mai

Tsadar mai: Gwamnatin tarayya tayi karin haske game da karin kudin mai

Hukumar nan dake sa ido wajen kayyade farashin man fetur ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPRA) a turance ta bayyana cewa babu wata maganar karin kudin mai da take shirin yi kamar yadda labarin hakan ke yawo cikin gari.

Hukumar dai ita ce ke da alhakin kayyade tare da kuma sa ido wajen ganin an bi ka'idar sayar da mai a farashin da ya dace tayi wannan karin haske ne a jiya cikin wata sanarwa da ta fitar ta kuma rabawa manema labarai biyo bayan dogayen layukan mai da suka fara bayyana a wasu sassa na kasar nan.

Tsadar mai: Gwamnatin tarayya tayi karin haske game da karin kudin mai

Tsadar mai: Gwamnatin tarayya tayi karin haske game da karin kudin mai

KU KARANTA: Buhari ya fitar da 'yan fursuna 500 a Kano

Legit.ng dai ta samu cewa sanarwar da ke dauke da sa hannun babban sakataren hukumar Mista Abdulkabir Sa'idu ta kuma kara jaddadawa dukkanin 'yan Najeriya cewar su kwantar da hankalin su su bar sayen man suna boyewa don kuwa an kawo karshen matsalar.

Daga karshe ne kuma sai sanarwar ta kara da cewa hukumar zata cigaba da bibiyar gidajen mai a fadin kasar don tabbatar da cewar an sayar da man a kan farashin da aka kayyade na Naira 145.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Legit Nigeria

Online view pixel