Nigerian news All categories All tags
Siyasa tamkar kasuwanci ne Inji Atiku Abubakar

Siyasa tamkar kasuwanci ne Inji Atiku Abubakar

- Atiku Abubakar ya kamanta siyasa da harkar kasuwanci

- Babban ‘Dan siyasar yana da niyyar tsayawa takara a 2019

- Jama’a sun yi watsa-watsa da Atiku game da kalaman na sa

Kwanaki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya gamu da fushin jama’a bayan da ya kamanta harkar siyasa da kasuwanci a shafin sa na Tuwita. Bisa duk alamu ‘Dan siyasar yana da niyyar tsayawa takara a zaben 2019.

Siyasa tamkar kasuwanci ne Inji Atiku Abubakar

Atiku yana ganin shi ya dace da mulkin Najeriya

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Jama’a a shafin Tuwita. ‘Dan siyasar da ya bar Jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP mai adawa kwanan nan yace babu banbamci tsakanin kasuwanci da kuma harkar siyasa.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya jinjinawa Shugaban Jam’iyyar PDP Makarfi

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriyar ya fadawa wani Bawan Allah mai suna Tayo Oviosu wanda yake ganin bai dace a kuma zaben Atiku ba, yana cewa siyasa da kasuwanci duk daya ne don kuwa kowa na kokarin saida hajar sa ne ga Jama’a.

Atiku dai yana ganin kowa na kokarin tallata hajjar sa ne domin a saye duk wanda aka ga dama. Mutane dai sun ce hakan na nufin Atiku kasuwanci kurum zai yi da ‘yan kasar don ana ganin yana cikin wadanda su ka jefa kasar cikin matsala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel