Nigerian news All categories All tags
Ziyarar Buhari jihar Kano: Sarki Sunusi ya yi ma Buhari gugar zana

Ziyarar Buhari jihar Kano: Sarki Sunusi ya yi ma Buhari gugar zana

A yau ne rana na biyu na ziyarar aiki na kwanaki biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar Kano, inda ya kaddamar da manyan ayyuka a jihar da kuma ganawa da al’ummar jihar.

Dayake da isar shugaba Buhari jihar, sai da ya leka fadar masarutar Kano, inda ya kai ma Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu gaisuwa, tare da nuna gadiyarsa da kokarin da masarautar Kano ke yi.

KU KARANTA: 2019: Buhari, ya hangi nasara a jihar Kano sakamakon fitar farin ɗango da dubun dubatan Kanawa suka yi don tarbarsa

Sai dai Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarki yayi wasu maganganu da bahaushe ka iya ce ma ‘Jurwayi mai Kaman wanka’, ko kuma a ce masa ‘Gugar zana.’

Ziyarar Buhari jihar Kano: Sarki Sunusi yayi masa Buhari gugar zana

A fadar Sarki

Sarkin ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa a ranar Laraba 6 ga watan Disamba, indaa ya bukaci Buhari ya dawo a badi don kaddamar da ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.

“Fatan mu shi ne a shekara mai zuwa, za ka zo ka kaddamar da manyan ayyukan gwamnatin tarayya a jihar Kano, kwantankwacin yadda ka zo ka kaddamar da ayyukan gwamnatin jiha ta yi a bana.” Inji Sarki Sunusi.

A na sa ran a yau ne shugaba Buhari zai kammala ziyarar aiki na kwanaki biyu daya kawo jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel