Nigerian news All categories All tags
Kungiyar NUPENG tayi tonan silili akan masu hannu wajen kawo karancin man fetur a kasar nan

Kungiyar NUPENG tayi tonan silili akan masu hannu wajen kawo karancin man fetur a kasar nan

Kungiyar ma'aikatan man fetur ta NUPENG (Nigeria Union of Petroleum Workers) ta danganta karancin man fetur da yake ta'azzara a kasar nan da wasu jiga-jigai na sashen kula da harkokin man fetur a kasar.

Kungiyar ta bayyana cewa, direbobin tankuna masu dakon man fetur ba su shiga wani yajin aiki ba da ake ta yada jita-jita a kasar nan.

A wata sanarwa ta ranar Larabar da ta gabata da kungiyar tayi ta bayyana cewa, mambobin kungiyar ba su da hannu wajen kawo karancin man fetur da ma'adanan sa da ake ta fama dashi a kasar nan.

Kungiyar NUPENG tayi tonan silili akan masu hannu wajen kawo karancin man fetur a kasar nan

Kungiyar NUPENG tayi tonan silili akan masu hannu wajen kawo karancin man fetur a kasar nan

A cewar shugaban kungiyar, Mista Igwe Achesa, bangare kungiyar masu dakon man fetur ta PTD (Petroleum Tanker Drivers) wadda take karkashin kungiyar NUPENG, suna nan a bakin aikin su na ci gaba da jigilar man fetur a lunguna da sako dake fadin kasar.

KARANTA KUMA: Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

Legit.ng ta fahimci cewa, sanarwar kungiyar ta kuma nuna rashin jin dadin ta dangane da gudanarwa masu kawo tsare-tsare a kasar nan akan rashin nuna ko oho ga bukatunta na gyara matatun man fetur hudu na kasar domin ci gaba da aikace-aikace a cikin su.

Kungiyar NUPENG ta kara jaddada cewa, jiga-jigai dake kula da harkokin man fetur a kasar nan suke da alhakin kawo cikas da koma baya ga yunkurin wadatar da man fetur a kasar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel