Nigerian news All categories All tags
Bankin duniya zata baiwa Najeriya bashin naira biliyan 360 domin inganta wutan lantarki

Bankin duniya zata baiwa Najeriya bashin naira biliyan 360 domin inganta wutan lantarki

- Bankin duniya ta bayyanawa kudirin ta na baiwa Najeriya bashin naira biliyan 360 domin inganta wutan lantarki

- Bankin duniyan tace a shirye take wajan taimakawa Najeriya farfado ta sashin wutan lantarkin nata

- Bankin duniyan ta nuna gamsuwarta kan nasarorin da gwamnatin Najeriya take samu a fanin samar da wutan lantarkin

A jiya Laraba 6 ga watan Disamba ne Bankin Duniya ta bayyana aniyar ta na baiwa Najeriya bashin kudi naira biliyan 360 domin bunkasa fanin samar da wutan lankarki.

A wajen taron da jami'an gwamnatin gwamnatin tarayya sukayi da takwarorinsu na Bankin duniyan, Bankin duniyan tace a shirye take wajen taimakawa Najeriya farfado da fanin samar da wutan lankarki a kasar.

Bankin duniya zata baiwa Najeriya bashin naira biliyan 360 domin inganta wutan lantarki

Bankin duniya zata baiwa Najeriya bashin naira biliyan 360 domin inganta wutan lantarki

Jami'an 2 sun amince da cewa akwai tanade-tanaden da ya kamata ayi kafin a mika bukatar na Najeriya ga mahuntar Bankin na duniya.

DUBA WANNAN: Wasu miyagu cikin gwamnati ne suka hadasa karancin man fetur, Inji NUPENG

Wata sanarwa da tawagar Bankin duniyan ta bayar a wurin taron ya nuna cewa sun gamsu da irin kokarin da jajircewa da gwamnatin tarayya take yi wajen ganin tayi gyara a fanin samar da wutan lantarkin.

"Bankin duniya a shirye take don tayi hadin gwiwa da kwamitin gwamnatin Najeriya da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa domin farfado da fanin wutan lantarki a kasar.

"Bankin duniyar zata cigaba da shirye-shiryen samar da bashin dallan Amurka biliyan 1 (naira biliyan 360) domin taimakawa gwamnatin Najeriya. Bankin duniyan da Najeriya sun amince da cewa akwai wasu tanade-tanade da za'a yi kafin a gabatar da kudirin bashin ga mahukunta Bankin duniyan," Inji sanarwar

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel