A karshe na kare a gidan kaso bayan na jefa wasu da dama akan aikata laifukan rashawa - Shugaba Buhari

A karshe na kare a gidan kaso bayan na jefa wasu da dama akan aikata laifukan rashawa - Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tunano tsawon shekarun da ya shafe a gidan kurkuku a lokacin mulkin soja a Najeriya.

Idan mai karatu bai manta ba, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya jefa shugaba Buhari a gidan kaso tun a shekarar 1985 har na tsawon sama da shekaru biyu.

A yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaba Buhari ya kai jihar Kano a ranar Larabar da ta gabata, shugaban yayi ikirarin cewa, sai da ya kasance ya kare a gidan kaso bayan ya jefa da dama sakamakon laifukan da suka aikata da ya danganci cin hanci da kuma rashawa.

Sai dai shugaba Buhari ya nemi al'ummar Najeriya da su fahimci banbance-banbance na tsarin mulkin soja da tsarin mulkin demokuradiya na farar hula.

Shugaba Buhari a yayin ziyarar jihar Kano

Shugaba Buhari a yayin ziyarar jihar Kano

Ya ci gaba da jawabi da cewa, yana mai kara janyo hankulan 'yan Najeriya akan su ci gaba da hakuri da juriya akan yanayin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki a halin yanzu, inda yace bayan "wuya sai dadi".

A kalaman sa, "ba abu ne mai sauki mu kawar da duk kalubalen dake gaban mu faraddaya ba, sai dai ya kamata mu fahimci dukkan mai nema yana tare da samu kuma bayan wuya sai dadi, saboda haka 'yan Najeriya su ci gaba da juriya wajen yin hakuri."

KARANTA KUMA: Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma hikaito wa 'yan Najeriya yadda ya kalubalanci sakamakon zabubbukan da suka gabata a shekarun 2007 da 2011.

Legit.ng ta ruwaito da sanadin shugaban inda yake cewa, ya dandana radadin neman kujerar shugabanci, domin kuwa sanin kowa ne ya tsaya takara har sau uku a shekarun 2003, 2007 da kuma 2011, sai dai bai yi nasara ba sai a karo na hudu a shekarar 2015.

Hakan ya sanya shugaba Buhari shiga kotu har na tsawon watanni 30 domin kalubalantar sakamakon zaben 2007 da kuma wasu watanni 16 da ya shafe wajen ziyarar kotu domin kalubalantar zaben 2011.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel