Buhari ya ziyarci Kano, ya jaddada alkawarinsa na murkushe yan ta’addan Boko Haram

Buhari ya ziyarci Kano, ya jaddada alkawarinsa na murkushe yan ta’addan Boko Haram

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki na kwanaki biyu a Kano ya jadadda jajircewarsa wajen kawo karshen yan ta’addan Boko Haram

- Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta maida hankali wajen yakar rashawa, ta’addanci da kuma daidata tattalin arziki

- Sarki Sanusi y aba shugaban kasar tabbacin samun goyon bayan masarautarsa a gwamnatinsa

A ranar Laraba, 6 ga watan Disamba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyace gwamnatinsa ta mayar da hanakli wajen yakar cin hanci da rashawa, kawo karshen ta’addanci da kuma daidaita tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kamfanin Dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Shugaban kasar ya ci gaba da cewa Kano ta kasance cibiyar cikini a arewacin Najeriya kafin yan ta’addan Boko Haram su gurgunta tattalin arzikin ta.

Buhari ya ziyarci Kano, ya jaddada alkawarinsa na murkushe yan ta’addan Boko Haram

Buhari ya ziyarci Kano, ya jaddada alkawarinsa na murkushe yan ta’addan Boko Haram

Ya yi alkawarin dawo da martabar birnin ta hanyar rushe ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

a nashi bangaren sarkin, ya ba shugaban kasar tabbacin cewa masarautarsa zata dunga taimaka masa da shawarwari masu amfani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel