Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

- Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

- An rahoto cewa Ademola ya ajiye wasikar murabus din nasa ne a ranar Laraba bayan ya jagorance shari’a guda hudu

- A baya ya sanya wani shari’a a yau, 7 ga watan Disamba, inda zai yanke hukunci

Justis Adeniyi Ademola, wanda hukumar DSS ta kama tare da sauran alkalai bakwai a 2016, yayi murabus daga babban kotun tarayya da kansa.

A cewar wata majiya na Vanguard Ademola, ya ajiye wasikar murabus din nasa ne a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, bayan ya jagoranci shari’a guda hudu.

Ku tuna cewa Ademola ya taba shiga wata badakalar rashawa a farkon shekarar nan sannan kuma kungiyar alkalan Najeriya (NJC ) ta dakatar da shi, kafin ya dawo bakin aiki a watan Yunin 2017.

Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

Justis Ademola ya yi murabus daga kujerar sa

A watan Janairu, wani jami’in hukumar DSS yayi amanna kan cewa an gano kudi naira miliyan 38, bindigogi biyu da wasu kudaden waje a gidan Ademola lokacin wani bincike da aka gudanar a gidansa a watan Oktoba, 2016.

KU KARANTA KUMA: IBB ya yi magana kan taron PDP, da sauya shekar Atiku

Justis Ademola bai ba da dalili na yin murabus din nasa ba cikin gaggawa sannan kuma ya sanya ranar wani zama a yau, 7 ga watan Disamba, domin yanke hukunci a kan wani shari’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel