PDP ta zargi APC da shirya makirci don rushe taron da zata gudanar

PDP ta zargi APC da shirya makirci don rushe taron da zata gudanar

- PDP ta zargi APC da shirya makirci domin rushe babban taron da jam’iyyar zata gudanar a ranar Asabar

- PDP na kokarin ganin ta dawo da tsofaffin jam’iyyarta da suka sauya sheka daga PDP a 2014

- Jam’iyyar ta ce tana duk wani kokarinta wajen ganin ta dawo da Saraki da tsofaffin gwamnonin da suka sauya sheka zuwa APC

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da shirya makirci don rushe babban taron da jam’iyyar ke shirin gudanarwa a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba.

Jaridar Nation ta ruwaito cewa PDP ta ce akwai wasu jami’ai a gwamnatin Buhari dake shirin hargitsa babban taron da zata gudanar sannan kuma tayi kira ga shugaban kasar da ya shigo lamarin sannan kuma ya dakatar da su.

PDP ta zargi APC da shirya makirci don rushe taron da zata gudanar

PDP ta zargi APC da shirya makirci don rushe taron da zata gudanar

Shugaban kungiyar amintattu na PDP, Walid Jibrin, yace jam’iyyar na duba zuwa ga tarban shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso zuwa PDP.

KU KARANTA KUMA: Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa

Jibrin ya kuma bayyana cewa Jam’iyyar na duba zuwa ga dawowar gwamnoni da suka sauya sheka a 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel