Mugun halin shugaban APC ya sa Atiku ya fice daga jam'iyyar - Timi Frank

Mugun halin shugaban APC ya sa Atiku ya fice daga jam'iyyar - Timi Frank

- Frank ya ce Oyegun bashi da hurumin sukar Atiku akan ficewar sa daga jam'iyyar APC

- Rashin iya shugabanci Oyegun yasa Atiku ya fita daga jam'iyyar APC inji Timi Frank

- Ficcewar Atiku da zaman sa a APC bashi da wani muhimmanci a wurin mu cewar Oyegun

Mataimakin sakataren yada labaru na jam’iyyar APC na kasa kuma jigo a jam’iyyar APC reshen jihar jihar Bayelsa Timi Frank, yace kalaman da shugaban jam’iyyar APC, Oyegun yayi akan Atiku bayan ya fice daga jam’iyyar APC bai da ce ba.

Timi Frank ya ce Oyegun bashi da hurmin sukar Atiku saboda ya fice daga jam’iyyar APC kuma kalaman sa yayi kama da na yan tasha.

Mugun halin shugaban APC ya sa Atiku ya fice daga jam'iyyar - Timi Frank

Mugun halin shugaban APC ya sa Atiku ya fice daga jam'iyyar - Timi Frank

A wata takarda da Timi Frank ya raba wa kafafen yada labaru, Frank ya rubuta cewa rashin iya shugabancin Oyegun yasa Atiku ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP.

KU KARANTA : Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun ya fito kafafen watsa labaru yace ficewar Atiku da tsayawar sa ba ta da wani muhimmanci ga jam’iyyar APC.

Amma Frank yace, “Da shugaban APC ya na da tunani , zaman takaici da damuwa yakamata yayi akan ficewar Atiku ba sukar sa ba,".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel