Nigerian news All categories All tags
IBB ya yi magana kan taron PDP, da sauya shekar Atiku

IBB ya yi magana kan taron PDP, da sauya shekar Atiku

- Ibrahim Babangida yayi magana game da sauya shekar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa PDP, da kuma babban taro na jam’iyyar adawa da za’a gudanar

- IBB ya nuna karfin gwiwa cewa kungiyar shirye-shirye karkashin Ifeanyi Okowa zasu isar da daya daga cikin taro mafi inganci da aka taba yi

- Ya kuma bayyana cewa an bari Atiku na sauya sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya kamar yadda ya so, sannan cewa babu aibu cikin sauya shekar sa

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, ya bayyana zuciyarsa akan babban taro na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da za’a gudanar, da kuma sauya shekar Alhaji Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar adawa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Babangida ya yi sharhin sa ne a lokacin da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa , shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi da sauran manyan jam’iyyar suka kai maa ziyarar ban girma, a gidansa dake Minna Hilltop, a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba.

IBB ya yi magana kan taron PDP, da sauya shekar Atiku

IBB ya yi magana kan taron PDP, da sauya shekar Atiku

Legit.ng ta tattaro cewa IBB ya nuna karfin gwiwa cewa kungiyar shirye-shirye karkashin Ifeanyi Okowa zasu isar da daya daga cikin taro mafi inganci da aka taba yi.

KU KARANTA KUMA: kasar Amurka na kokarin ingiza sabon yaki a tsakanin kasashen Larabawa kan birnin Qudus

Da yake magana akan sauya shekar Atiku, ya bayyana cewa: “Shi dan Najeriya ne, an bashi damar zuwa duk jam’iyyar da yake so sannan kuma kundin tsarin mulkinmu ya yarda da hakan, don haka ba sabon abu bane, sannan kuma babu wani aibu don dan siyasa ya sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel