Nigerian news All categories All tags
Kai Jama'a: An sacewa wani mutumi sama da Naira Miliyan 600 a banki

Kai Jama'a: An sacewa wani mutumi sama da Naira Miliyan 600 a banki

- Wani Ma’aikacin banki ya sace miliyoyin kudin wani mutumi

- Ma’aikacin yace Mahaifin sa ne ke jinya ya sa yayi wannan aiki

- Alkali mai shari’a ya bada belin sa kan kudi N100,000 a yanzu

An sacewa wani mutumi sama da Naira Miliyan 620 a wani banki. Yanzu haka har maganar ta kai an shiga Kotu da wanda ake zargi da wannan mugun aiki. Ma’aikacin yayi kukan cewa Mahaifin sa ne ke jinya ya sa yayi haka. Yanzu dai an bada belin sa.

Kai Jama'a: An sacewa wani mutumi sama da Naira Miliyan 600 a banki

Ma’aikacin banki ya shiga Kotu bayan ya saci kudin wani

An maka wani Ma’aikacin bankin Wema mai shekaru kusan 30 a Duniya mai suna Shola Adeyami a Kotu bayan ya yi gaba da Miliyan 625 na wani mutumi mai suna Michael Asanba da ke adana kudin sa a babban bankin da ke Garin Legas Inji Punch.

KU KARANTA: An damke wani Alkali yana neman rashawar Miliyan 20

Adeyemi dai zai amsa zargin da ke kan sa na yin kutun-kutun da kuma satar kudi a gaban Kotun Majistare da ke Unguwar Igbosere da ke Garin na Legas. Ana tunani wannan Matashi ya kirkiri sa hannun Mista Asanba ne yayi gaba da kudin sa.

Lauyan wanda ake zargi yace dole ce ta sa ya saci wannan kudi daga asusun Micheal Asanba saboda Mahaifin sa na fama da rashin lafiya. Sai dai babu wata shaida da ta nuna cewa Mahaifin na sa bai da lafiya kuma ba mamaki ya dandana kudar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel