Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa

Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa

- Matasan Niger Delta sun yi kira ga Atiku da karda ya tsaya takara a 2019

- Sun bukaci da ya nemi matsayar shugabanci a PDP

- Matasan sun caccaki Sanata Ben Bruce kan nuna goyon baya ga kudrin Atiku na neman shugabancin kasa

Wata kungiyar matasan Niger Delta sun caccaki Sanata Ben Murray-Buce kan goyon bayan kudirin Alhaji Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Vanguard ta rahoto cewa a wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Harry Lawson da sakatare Preye Wilson a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba, kungiyar tace Goodluck Jonathan ya fadi zabe a 2015 saboda Atiku.

Yayinda suke yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar maraba da dawowa PDP, kungiyar tace ya nemi matsayar shugabancin jam’iyyar maimakon neman shugabancin kasa.

Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa

Matasan Niger Delta sun bukaci Atiku da karda ya tsaya takarar shugabancin kasa

A halin yanzu, kungiyar amintattu na PDP sunyi kira ga mambobinsu da suka bar jam’iyyar da su koyi da Atiku sannan su dawo gida.

KU KARANTA KUMA: Allah zai hukunta wadanda suka sace dukiyan Najeriya – Shugaba Buhari

NAN ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, sanata Walid Jibrin, yayi wannan kira ne yayinda yake zantawa day an jkarida a ranar Laraba a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel