Abun da shugaba Buhari ya fadawa sarkin Kano, Sanusi na II

Abun da shugaba Buhari ya fadawa sarkin Kano, Sanusi na II

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wa jihar Kano ziyara na kwana 2

- Buhari ya fadawa sarkin Kano cewa babu wanda zai iya bata shi wajen yan Najeriya akan kyakawan manufar ga wannan kasa

- Shugaba Buhari ya ce jihar Kano ce cibiyar zaman lafiya da kasuwanci a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II cewa babu wanda zai iya bata shi wajen yan Najeriya akan kyakawan manufar sa ga yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe a 2015.

Hadimin shugaban kasa na fannin watsa labaru Garba Shehu ya bayyana haka.

Buhari ya fadawa sarkin Sanusi hakane a lokacin da ya kai wa jihar Kano ziyarar na kwana biyu a ranar Laraba.

Abun da shugaba Buhari ya fadawa sarkin Kano, Sanusi na II

Abun da shugaba Buhari ya fadawa sarkin Kano, Sanusi na II

Ya kara da cewa "Abubuwan uku muka ce zamu gyara a lokacin yakin neman zabe wanda ya kunshi, tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, kuma babu wanda zai iya karkatar da hankulan yan Najeriya akan kyakwan manufar mu ga wannan kasa.

KU KARANTA : Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

Shugaban kasa yayi alkawarin cewa zai tabbatar da gwamnatin sa ta kawu karshen ta’adancin yan kungiyar Boko-haram.

Kuma nasarar da aka samu a fannin tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa ba zai tsaya ba.

Buhari yace "jihar Kano cibiyar zaman lafiya da kasuwanci ne a Najeriya, saboda haka idan aka samu matsala a Kano kamar kasar baki daya ta samu matsala.

Shugaban kasa yace "ya tuna yadda rashin tsaro ayanki Arewa maso gabas ya janyo wa kamfanonin jihar Kano cikas a baya,".

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel