Nigerian news All categories All tags
Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

A ranar Litinin din da ta gabata ne tsananin bashi ya sanya wani dattijo mai shekaru 57 a duniya ya kashe kan sa ta hanyar rataya a birnin Ibadan dake jihar Oyo.

Wannan lamari dai ya faru ne yayin da dattijon mai sunan Olajire Otunla, wanda ke zaune a gida mai lamba SW8/634 na unguwar Oke-Ado a birnin Ibadan ya jefa al'ummar dake makwabtaka da shi cikin zulumi.

Da misalin karfe 1:30 na ranar Litinin din da ta gabata, bayan dawo wa daga cin kasuwa na uwargidan marigayin, Misis Minisola Otunla, sai ta nufi turakar su domin ta sauke gajiyar ta kafin ta koma kan aikace-aikacen gida.

Isar ta kofar dakin ke da wuya sai ta iske ta a garkame kuma tayi bugun duniya amma ta ji shiru, hakan ya sanya ta gayyato makwabta aka balle kofar, sai kwatsam suka yi kacibus da gawar mai gidan ta sargafe da igiya tana reto a jikin taga.

Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

Nauyin bashi na Naira 300, 000 ya sanya wani dattijo ya rataye kansa a birnin Ibadan

Uwargidan marigayin ta shaidawa manema labarai cewa, mijin ta mutum ne mai halaye na gari, sai dai babban abin da zai sa yayi sanadin ajalin sa shine nauyin bashi na Naira 300, 000 da yayi masa katutu.

KARANTA KUMA: Ban bi sahun mahaifina zuwa jam'iyyar PDP ba - Inji 'yar Atiku

Daya daga cikin 'ya'yan marigayin Bolade Otunla ta bayyana cewa, tayi matukar mamakin samun rahoton wannan danyan hukuncin da mahaifin na su yayi.

Legit.ng ta fahimci cewa, marigayin ya rasu ya bar 'ya'ya hudu; maza biyu da mata biyu wanda duk sun mallaki hankalin kan su.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel