Wasu miyagu cikin gwamnati ne suka hadasa karancin man fetur, Inji NUPENG

Wasu miyagu cikin gwamnati ne suka hadasa karancin man fetur, Inji NUPENG

- Kungiyar NUPENG tace bata da hannu wajen hadasa karancin man fetur a wasu sassan kasar nan domin mambobin su basu tafi yajin aiki ba

- Shugaban kungiyar yace wasu miyagu cikin gwamnati suka haifar da matsalar domin sun ki gyara matatun man fetur 4 da ke Najeriya

- Kungiyar tayi kira da gwamnatin tarayya tayi gagawan magance matsalar domin mutane su gudanar da shagulgulan su walwala

Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskan gas na kasa NUPENG ta daganta karancin man fetur da ya mamaye sassan kasan nan cikin kwanaki biyun nan a matsayin aikin wasu miyagu da ke cikin gwamnati.

A sanarwan da kungiyar NUPENG ta fitar jiya, yace mambobin kungiyar basu da hannu cikin halin karancin man fetur din da kasar ke fuskanta.

Wasu miyagu cikin gwamnati ne suka hadasa karancin man fetur, Inji NUPENG

Wasu miyagu cikin gwamnati ne suka hadasa karancin man fetur, Inji NUPENG

A cewar shugaban kungiyar, Mista Igwe Achese, direbobin kungiyar suna dakon man fetur zuwa lunguna da sakunnan kasar nan kamar yadda suka saba kuma kungiyar tasu bata yajin aiki.

KU KARANTA: Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

Yace karancin man fetur din ya faru a dalilin rashin gyara matatun man fetur 4 da Najeriya ke dashi duk da cewa sun jawo hankalin masu ruwa da tsaki a fanin a kan gudanar da haka.

Shugaban kungiyar yayi kira da gwamnatin tarayya ta gagauta warware matsalar domin saukaka ma al'umma musamman a wannan lokacin shagulgula da muke fuskanta.

KU KARANTA: An damke wani Alkali bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel