Nigerian news All categories All tags
kasar Amurka na kokarin ingiza sabon yaki a tsakanin kasashen Larabawa kan birnin Qudus

kasar Amurka na kokarin ingiza sabon yaki a tsakanin kasashen Larabawa kan birnin Qudus

- Shugaban kasar Amurka ya mayar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Israila

- Yin hakan na iya haddasa yaki tsakanin kasashen Larabawa

- An kuma zargi Trump da kwanto kura

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin Amurka karkashin shugaban kasa Donald Trump na kokkarin kokarin tayar da zaune tsaye a kasashen Larabawa bayan Trump ya mayar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Israila.

A yayinda yake jawabi a fadar White House Shugaba Trump, ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri da aka dade ba’a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Okorocha ya ga ta kan sa bayan ya nada Kwamishinar jin dadi a Imo

Sai dai kuma Kungiyar Hamas ta kalubalanci labarin inda ta bayyana cewa shugaba Donald Trump ya kwanto kura.

An nasa martanin, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana halin da ake ciki a matsayin zaman zullumi inda ya ce babu wani zabi daya wuce a samar da kasashe biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel