Nigerian news All categories All tags
2019: Buhari, ya hangi nasara a jihar Kano sakamakon fitar farin ɗango da dubun dubatan Kanawa suka yi don tarbarsa

2019: Buhari, ya hangi nasara a jihar Kano sakamakon fitar farin ɗango da dubun dubatan Kanawa suka yi don tarbarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gode da irin tarbar da Kanawa suka nuna masa a yayi ziyarar kwanaki biyu daya fara a ranar Laraba 6 ga watan Disamba, inji rahoton Daily Trust.

A yayin jawabinsa a fadar Sarkin Kano, Buhari yace ganin dimbin jama’n da duka yi masa maraba a jihar, ya nuna cewa zai iya sake cin jihar Kano a kakar zabe ta shekarar 2019.

KU KARANTA: Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun kunnen ƙashi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari na cewa “Na yi mamaki matuka da irin jama’an da suka fito tarba ta, wannan na nuni da zamu iya cin zabe a jihar Kano, haka zalika hakan na nufin Kanawa na sane irin kokarin da muka yi musu a fannin tsaro da noma.”

2019: Buhari, ya hangi nasara a jihar Kano sakamakon fitar farin ɗango da dubun dubatan Kanawa suka yi don tarbarsa

Buhari a fada

Buhari ya cigaba da fadin “Mun samu nasarori a kokarin mu an cika alkawurran muka dauka da suka hada da tsaro, tattalin arziki, da kuma yaki da rashawa. a yanzu haka hadakan kasashen Nijar, Chadi da Najeriya sun samu galaba a kan Boko Haram.”

Shugaba Buhari yace zaman lafiya a yankin Arewa na da matukar tasiri a Najeriya gaba daya, ta yadda idan Arewa ta zauna lafiya, toh Najeriya ma ta zauna lafiya kenan, hakazalika idan akwai matsala a Arewa, Najeriya ma bata da lafiya kenan.

Dayake jawabi kan bambamcin mulkin Soja da na farar hula, Buhari yace “A lokacin da nake mulkin Soja, na kama mutane da dama, a kan zargin cin hanci da rashawa, daga karshe ni ma na kare a Kurkuku. Amma tun daga 1994-2014, gwamnatin Najeriya ta samu kudi, sai dai an yi bindiga da su.”

Daga karshe Buhari ya yaba ma masarautar Kano, inda yace duk abin da ya zama a rayuwarsa, ya zama ne a dalilin gudunmuwa daya samu daga masarautar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel