Gwamna Okorocha ya ga ta kan sa bayan ya nada Kwamishinar jin dadi a Imo

Gwamna Okorocha ya ga ta kan sa bayan ya nada Kwamishinar jin dadi a Imo

- Gwamnan Jihar Imo ya gamu da suka iri-iri daga bakin Jama’a

- Okorocha ya nada kanwar sa a matsayin Kwamishinar jin dadi

- Gwamna Rochas dai takarar Shugaban Kasa ma ya ke shirin yi

Tun ba yau ba aka taba cewa ya kamata a rika yi wa Shugabannin Najeriya gwajin kwakwalwa don ba mamaki su na fama da tabin hankali saboda irin abin da su ke yi a kan mulki. Kwanaki Gwamnan yayi ta gina gumukan wasu manyan Shugabanni.

Gwamna Okorocha ya ga ta kan sa bayan ya nada Kwamishinar jin dadi a Imo

Rochas Okorocha ya kashe rabin biliyan wajen gina mutum-mutumi

Kwanan nan wani na kusa da tsohon Shugaban Kasa Jonathan Goodluck mai suna Reno Omokri yayi kaca-kaca da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha. Omokri yace saboda irin su Gwamna Okorocha ya kamata ace ana duba lafiyar Shugabanni.

KU KARANTA: An yi ca a kan Gwamna Wike bayan ya kashe kudi kan wasu motoci

Gwamna Okorocha ya nada Kwamishinoni har 27 kuma ciki har da kanwar sa. Gwamnan kuma ya nada ta ne a matsayin kwamishinar jin dadin ma’aurata da kuma farin ciki a Jihar. Jama’a da dama dai sun soko wannan tsari na Gwamnan na Imo.

Reno Omokri yace ko dan irin su Gwamna Okorocha, ya kamata a rika yi wa ‘yan siysa gwaji kafin su dare kan mulki. A cewar Omokri, dole a binciki lafiyar wasu Shugabannin Kasar don kuwa akwai ‘yar matsala a cikin kwakwalwar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel