Nigerian news All categories All tags
Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Abdullahi Ganduje ta shirya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari liyafar cin abinci don girmama shi, kamar yadda Legit.ng ta gano.

An shirya wannan liyafa ne don gode ma shugaba Buhari da ziyarar da ya kai jihar ta Kano, irinsa a farko tun bayan daya dare madafan iko sama da shekaru biyu da suka wuce.

KU KARANTA: Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun kunnen ƙashi

Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

Liyafar

Wani ma’abocin kafar sadarwa zamani, Buhari Sallau ya daura hotunan a shafin sa na Facebook, inda aka hangi shugaba Buhari tare da Gwamnan Kano, Sarkin Kano, Gwamnan Jigawa da kuma mataimakin gwamnan jihar a zaune.

Yayin da sauran jama’a kuma ke ta kai kawo da kwanukan abinci ana, kulu wa sharabu, tare da nuna farin ciki da annushuwa.

Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

liyafar cin abinci

A ranar Laraba 6 ga watan Disamba ne dai shugaba Buhari ya fara ziyarar aiki ta kwana biyu jihar Kano, da nufin gode ma Kanawa game da goyon bayan da suka ba shi a zabukan 2019, haka zalika zai kaddamar da ayyukan jihar.

Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

Manyan baki

Gwamna Ganduje ya shirya ma shugaba Buhari kasaitaccen liyafar cin abinci

liyafar cin abinci

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel