Dansanda ya harbe wata ɗaliba da abokinta a kan cin hancin naira 1000

Dansanda ya harbe wata ɗaliba da abokinta a kan cin hancin naira 1000

Wani jami’in Dansanda dake ofishin Yansanda na garin Igbuzo, jihar Delta, mai suna Sajan Abua ya cika ma wandonsa iska bayan ya bindige wata dalibar kwalejin kimiyya da fasaha na jihar, har lahira.

Baya da daliba Safia Ogogo, dansandan ya harbe wani jami’in gwamnati, Victor Emeagwai a wani shingen duba ababen hawa dake garin Igbuzo, kamar yadda Punch ta ruwaito

KU KARANTA: Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun kunnen ƙashi

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da aka harba na cikin tafiya ne tare da wani abokinsa, Jerry Akinlabi a lokacin da suka iso wani shingen Yansanda, inda wani Dansanda dake wajen, Nwakolo ya nemi direban motar ya bashi cin hancin N200.

Shi kuma direban motar, Akinlabi ya hana, sa’annan ya zura a guje da motarsa, hakan ne ya harzuka Yansandan, inda suka bude ma motar wuta, suka samu buduwars Akinlabi, Sofia, da abokinsa, Emeagwai.

Maajiyar Legit.ng ta ruwaito tuni aka kama Yansandan su 3 da shugabansu, ASP Akhabue, bayan da Akinlabi ya kai karar su zuwa ga kwamishinan Yansanda, yayin da shi wanda ya bude wutar, Abua ya ranta a na kare.

Daga karshe an garzaya da mutanen su biyu zuwa Asibti, kuma yace kwamishinan ya biya kudin magani har Naira 10,000, kuma budurwar tasa da abokinsa sun fara samun sauki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel