Wata ɗaliba ta kai hankalin ta nesa, ta watsa ma abokinta ruwan zafi mai barkono

Wata ɗaliba ta kai hankalin ta nesa, ta watsa ma abokinta ruwan zafi mai barkono

Wani ɗalibin kiwon lafiya daga kwalejin horar da jami’an kiwon lafiya na garin Krosribas, Ethorti Uno ya gamu da tashin hankali yayin da wata kawarsa, Eteng Odinke, ta watsa masa ruwan zafi mai hade da yaji.

The Nation ta ruwaito Saurayin, ya samu mummunan kuna a kirjinsa, da cinya bayan da kawar tasa ta watsa masa ruwan, sakamakon ya yi mata nasiha kan irin mugun halin da take shi da kuma rashin ladabi da take nuna ma jami’an asibitin Abini, inda suke je don samun horo.

KU KARANTA: Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun kunnen ƙashi

Majiyar Legit.ng da dama daga cikin ma’aikatan Asibitin Abi sun koka kan halin yarinyar, don haka ne sai Ethorti, wanda shine shugaban daliban masu naman kwarewa dake wannan Asibiti ya nemi yayi mata nasiha.

Wata ɗaliba ta kai hankalin ta nesa, ta watsa ma abokinta ruwan zafi mai barkono

Odinge

Suna cikin magana sai Eteng ta yi tafiyarta zuwa daki, ash eta daura ruwa a kan wuta, yayin da ya tafasa, sai ta zuwa basa yaji, sa’annan ta fito cikin fushi, inda ta tunkari Ethorti ta watsa masa.

Da yake bayani a Asibiti, Ethort yace “Ina jan hankalin ta ne fa dangane da irin batutuwan da ake yi game da halayenta, sai kawai ta fara zagina tana neman yin fada da ni, amma sai abokanmu suna raba mu, shine fa ta tafi dakinta ta yin wannan aika aika.”

Tuni Yansandan jihar Calabar suka yi awaon gaba da Eteng, yayin da iyayen ta suka bukaci biyan kudin maganin Ethorti, daga yanzu har zuwa ya damu lafiya.

Ita ma shugaban tsangayar ilimin kiwon lafiya na kwalejin, Dakta Winifred Itam ta bayyana cewa zasu gudanar da bincike kan lamarin, sa’annan ta jaddada dacewar kowanne jami’in kiwon lafiya ya kasance mai halaye nagari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel