‘Yan Majalisar Amurka na shirin tsige Shugaban Kasa Trump

‘Yan Majalisar Amurka na shirin tsige Shugaban Kasa Trump

– An fara yunkurin tsige Shugaban Kasar Amurka Trump

– Wani ‘Dan Majalisar Kasar yace Trump bai cancanta ba

– 'Dan Majalisar ya rubuta takarda ga ‘Yan Jam’iyyar sa

Mun ji cewa a tsakiyar makon nan ne aka fara shirin sauke Shugaban kasar Amurka Donald J. Trump daga mukamin sa inda wasu ‘Yan Majalisar wakilai masu adawa ke ganin cewa bai cancanci mulkin Kasar ba. Sai dai hakan ba zai zo da sauki ba ko kadan.

‘Yan Majalisar Amurka na shirin tsige Shugaban Kasa Trump

Majalisar Wakilai na neman tsige Donald Trump

Wani ‘Dan Majalisar Kasar daga Jam’iyyar adawa ta Democrats ya bayyana cewa zai kawo kudirin tsige Shugaban Kasar a gaban Majalisa saboda ta tabbata tun ba yau ba cewa Shugaban bai san abin da yake yi ba, kuma bai san martabar kujerar sa ba.

KU KARANTA: Ko da gaske Abacha ya saci wadannan makukun kudi da ake kira?

Wasikar da wani ‘Dan Majalisar Kasar mai wakiltar Yankin Texas yake kokarin aikawa abokan aikin sa ta fito fili inda aka ga ya zargi Shugaba Donald Trump da nuna kiyayya da kuma jawo tashin hankali a matsayin sa na Shugaban na Kasar Amurka.

Sai dai wasu manyan ‘Yan Jam’iyyar adawar na ganin cewa bai dace a fara maganar tsige Shugaban ba yayin da ake bincike game da yakin neman zaben sa wanda idan an same sa da rashin gaskiya, a iya bin dokar kasa wajen sauke sa daga mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel