Nigerian news All categories All tags
Kotu ta dau zafi akan mutane 3 bisa laifin mallakar tabar wiwi

Kotu ta dau zafi akan mutane 3 bisa laifin mallakar tabar wiwi

A ranar Larabar da gabata ne wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Badagry, ta gurfanar da mutane uku a sakamakon aikata babban laifi na mallakar moli shida na tabar wiwi.

Legit.ng ta kawo muku sunaye wadannan mutane da sanadin jaridar Daily Post kamar haka; Chinonso Izueke, Oyam Raphael da Omokpia.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, Sufeto Akpam Ikem ya bayyana wa kotu cewa, mutane ukun sun aikata wannan laifin ne a ranar 29 ga watan Nuwamba a yankin marine na unguwar Badagry dake jihar Legas.

Jami'i Akpam ya bayyana cewa, masu ran gadi ne a wata mashaya suka cafke mutane ukun a yayin da suke cikin maye na zukar tabar wiwi, wanda hakan ya sanya suka mika su ga hukumar 'yan sanda.

Kotu ta dau zafi akan mutane 3 bisa laifin mallakar tabar wiwi

Kotu ta dau zafi akan mutane 3 bisa laifin mallakar tabar wiwi

Ya kara da cewa, wannan laifi da mutane ukun suka aikata ya saba wa dokar kasa ta gwamnatin tarayya karkashin sashe na 5.

KARANTA KUMA: Ban bi sahun mahaifina zuwa jam'iyyar PDP ba - Inji 'yar Atiku

Sai dai shi alkalin kotu, Mista Jimoh Adefioye, bai zartar da hukunci akan wadanda ake tuhuma ba, inda ya nemi su da biyan belin kowane daya daga cikin su akan kudi Naira 100,000 tare da gabatar da mutum uku da za su tsaya musu a matsayin jingina.

Alkali Jimoh ya kuma daga sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Janairu domin ci gaba da shari'a.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel