Nigerian news All categories All tags
An damke wani Alkali bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200

An damke wani Alkali bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200

- Hukumar ICPC ne ta damke alkalin bisa zargin neman rashawa

- Hukumar kuma ta fara bincike kan gidajen gwamnati da a ka sayar a zamanin Obasanjo

- Binciken ya faru ne sakamakon koken da 'yan Nijeriya masu kishin Kasa su ka gabatar

Hukumar yaki da rashawa da sauran almundahana (ICPC), ta damke Alkali Mohammed Tsamiya (Murabus), bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200 daga hannun Mista Nnamdi Orji, na Jihar Imo, don karkatar da nasarar shari'ar zabe gare shi.

An damke wani Alkali bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200

An damke wani Alkali bisa zargin neman rashawar naira miliyan 200

Wannan laifi da a ke zargin Tsamiya da aikata shi, ya faru ne a shekarar 2015. Sai dai kuma hukumar ta bayar da belin Alkali Tsamiya bayan ya cika sharuddan belin. Hukumar za ta cigaba da gudanar da bincike game da lamarin.

KU KARANTA: Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

Har ila yau, hukumar ta fara bincike kan gidajen gwamnati guda 24,325 da a ka sayarwa jami'an gwamnati a zamanin shugabancin Olusegun Obasanjo.

An fara wannan bincike ne sakamakon koken da 'yan Najeriya masu kishin Kasa su ka kai ga hukumar. Masu koken sun koka da yadda a ka sayar da wasu daga gidajen ba bisa ka'ida ba kuma ga wadanda ba su cancan ta ba.

Sun kuma kuka da yadda wadansu ma ba su biya kudin sayen ba har ya zuwa yanzun, a yayin da wadansu jami'an gwamnatin su ka ware wasu daga gidanjen su na bayar da haya. Hukumar dai ta samu ikon kwato naira 18,031,000 a halin yanzun, yayin da bincike ya cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel