Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun yi kunnen ƙashi

Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun yi kunnen ƙashi

Gwamnatin tarayya ta koka kan yadda da dama daga cikin wasu yan Najeriya suka yi kememe suka ki yarda a maido su gida daga kasar Libya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito Geoffrey Onyeama.

Mista Geoffrey Onyeama, wanda shi ne Ministan harkokin kasashen waje, ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin dayake ganawa da manema labaru bayan taron majalisa koli ta kasa.

KU KARANTA: Kotun ta yanke ma wasu yan Fyaɗe hukuncin ɗaurin rai da rai a jihar Bauchi

Onyeam ya kara da cwa sun gayyato jakadan Najeriya kasar Libya don yayi musu karin haske game da adadin yan Najeriya dake daure a sansanoni daban daban, ta yadda gwamnati za ta yi amfani da bayanansa don ceto wadadan suka rage.

Na ji daɗi ne gari: Wasu yan Najeriya dake ci-rani a kasar Libya sun kunnen ƙashi

A libya

Majiyar Legit.ng ta jiyo shi yana fadin gwamnati za ta yi amfani da hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, tare da hukumar yaki da fataucin mutane, NAPTIP don nemo hanyoyin bi wajen dawo da yan Najeriya gida.

“Da dama daga cikin yan Najeriyan basu da niyyar dawowa gida, don haka zamu dauko wadanda ke da burin dawowa ne kadai.” Inji Shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel