Nigerian news All categories All tags
An ba Hamid Ali da Emefiele kwanaki 7 su bayyana a gaban Majalisa

An ba Hamid Ali da Emefiele kwanaki 7 su bayyana a gaban Majalisa

– Hamid Ali da Gwamnan CBN za su bayyana a gaban Majalisa

– ‘Yan Majalisar Wakilai na bincike game da harkar shigo da kaya

– Bayan nan kuma za a nemi jin ta bakin babban Akantan Kasar

Labari ya zo mana cewa a makon nan ne Majalisar Wakilai ta Tarayya ta kira Shugaban Hukumar kwastam Hamid Ali da wasu manyan mukarraban Gwamnatin Tarayya da su bayyana gaban ta.

An ba Hamid Ali da Emefiele kwanaki 7 su bayyana a gaban Majalisa

Majalisar Wakilan Tarayya ta aikawa Hamid Ali da kira

Shugaban Kwastam na kasa Kanal Hamid Ali mai ritaya da Gwamnan babban bankin kasar na CBN Godwin Emefiele za su bayyana a gaban Majalisar Wakilan domin bada amsa game da yadda aka rika ba wasu dama su na shigo da kaya cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta gina kwalejin fasaha na Sojoji a Kaduna

Shugaban Kwamitin aikin kwastam a Majalisa Honarabul James Audu Faleke ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa sun ba Hamid Ali mako guda ya bayyana a gaban su domin yi masu bayani game da harkar shigo da kaya ta kan iyakokin Najeriya tun daga 2010.

Bayan nan kuma Majalisar za ta nemi jin ta bakin Akanta-Janar na kasar Mista Ahmed Idris. Majalisar Wakilan Kasar na zargin cewa akwai wadanda ake ba dama su shigo da kaya ba tare da bin ka’ida ba ko kuma yi masu alfarmar da bai dace ba cikin Kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel