PDP ta nuna ma Atiku wariya, ba zai jefa kuri’a a zaben shuwagabanninta ba

PDP ta nuna ma Atiku wariya, ba zai jefa kuri’a a zaben shuwagabanninta ba

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ba zai jefa kuri’a ba a ranar babban taron sun a kasa, inda za’a gudanar da zaben shuwagabannin jam’iyyar.

Jaridar Punch ta ruwaito Kaakakin jam’iyyar, Dayo Adeyeye yana fadin babu yadda za’a yi Aiku yayi zabe a ranar saboda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya hana sababbin shiga jam’iyyar jefa kuri’a, sai dai yace za’a bashi damar yin jawabi a ranar.

KU KARANTA: Kotun ta yanke ma wasu yan Fyaɗe hukuncin ɗaurin rai da rai a jihar Bauchi

Adeyeye ya bayyana haka ne a ranar Laraba 6 ga watan Disamba, a garin Abuja, inda yace “Abin ya dace shine mutum ya dauki dokokon dake cikin kundun tsarin mulkin jam’iyyar PDP, a nan za’a gane ko Atiku na iya yin zabe a ranar ko kuwa.

PDP ta nuna ma Atiku wariya, ba zai jefa kuri’a a zaben shuwagabanninta ba

Atiku

“Muna murna da dawowar Atiku, yana daya daga cikin jiga jigan jam’iyyar, don haka zamu gayyace shi zuwa babban taron mu na kasa, zai yi jawabi, amma ba lallai bane yayi zabe a ranar duba da, sashi na 2 (1) na kundin tsarin mulkin PDP.” Inji shi.

Sashi na 2 (1) na nuni da cewa duk mutumin daya dawo cikin jam’iyyar PDP ba zai samu damar jefa kuri’a ba, ko kuma ya tsaya takara don a zabe shi ba, tun da yana kamar yana karkashin talala ne har sai idan shugabannin jam’iyyar ne suka sahhale masa.

Sai dai majiyar Legit.ng ta kalato cewar jam’iyyar na shirin yi ma kundin tsarin mulkin nata kwaskwarima, don Atiku ya samu damar jefa kuri’ar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel