Champions league: Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo ya shiga tarihi

Champions league: Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo ya shiga tarihi

- Ronaldo ya kara kafa wasu tarihi a Gasar Champions League

- Dan wasan ya jefa kwallon sa na 114 a Gasar na Zakarun Turai

- Cristiano ya jefa kwallo a raga a duka wasannin rukunin bana

A jiya ne Babban Dan wasan nan na gaban Real Madrid Cristiano Ronaldo yayi abin da ba a taba yi ba a Gasar Champions League na Zakarun Nahiyar Turai a wasan su da Borrusia Dortmund a Birnin Madrid.

Champions league: Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo ya shiga tarihi

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya bar tarihi

A Gasar bana, Dan wasan ya kafa tarihi inda ya zama na farko a tarihin Duniya da ya taba zura kwallo a kowane wasa da Kungiyar sa ta buga a zagayen farko na rukuni. Ronaldo ya leka raga a duka wasanni 6 da Real Madrid ta buga wannan karo.

KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya fadi lokacin da zai yi ritaya da wasa

Dan wasan na Duniya mai shekaru 32 ya ci kwallon sa na 114 a Gasar na Turai. Duk Duniya babu wanda ya sha gaban Ronaldo a yawan kwallaye a Gasar na Champions league. Kwanan nan ake sa rai Ronaldo zai lashe kyautar Ballon D’or na Duniya.

Sai dai kuma a Gasar La-liga na gida, Dan wasan bai kai labari ba don kuwa kwallaye 2 rak ya iya ci bana cikin wasanni 10. A Gasar Turai kuwa ya jefa kwallaye kusan 9 cikin wasanni 6. Yanzu dai Real Madrid ta isa zagaye na gaba a Gasar na Turai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel