Gwamnatin Tarayya za ta gina kwalejin fasaha na Sojoji a Kaduna

Gwamnatin Tarayya za ta gina kwalejin fasaha na Sojoji a Kaduna

– Gwamnatin Shugaba Buhari za ta gina wasu kwalejin karatu

– Buhari ya sa hannu a kudirin biyan fansho ga Hukumar NIA

– Daga ciki har da kwalejin fasaha na Sojojin saman Najeriya

Labari ya zo mana cewa a makon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu kudirori har 3 wanda za su bada dama Gwamnatin Tarayya ta gina wasu makarantun koyon aiki na Soji.

Gwamnatin Tarayya za ta gina kwalejin fasaha na Sojoji a Kaduna

Buhari ya sa hannu a wasu muhimman kudirori

Kamar yadda mai ba Shugaban Kasar shawara wajen yada labarai Femi Adesina ya bayyana, Shugaba Buhari ya tafka hannu a kudirori wanda daga ciki akwai na gina kwalejin koyon likitancin hakori na Gwamnatin Tarayya a Garin Enugu.

KU KARANTA: An nemi Minista Kachikwu ya kawo karshen wahalar mai

Bayan nan kuma Shugaba Buhari ya amince da gina wata tsangaya ta koyon fasaha na Sojojin saman Kasar. Gwamnatin Tarayya za ta gina wannan makaranta ne a Garin Kaduna inda Makarantar Sojin saman Kasar ta ke a yanzu.

A wadannan makarantu dai za a rika yin Digiri, da difloma da ma takardar shairdar satifiket har daga sauran kasashen Duniya. Shugaban ya kuma sa hannu a kudirin da zai ba Hukumar NIA na tsaron kasa damar samun fansho bayan ritayan Jami’an su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel