Rikicin makiyaya a jihar Cross Ribas ta tilasta wa mazaunar fiye da 300 barin gidajensu

Rikicin makiyaya a jihar Cross Ribas ta tilasta wa mazaunar fiye da 300 barin gidajensu

- Akalla fiye da mazauna 300 sun gudu daga gidanjensu bayan da Fulani suka mamaye garin su

- Makiyayan sun yi tsayayya ga ƙoƙarin da mazaunar garin suka yi don hana su shiga gonakin su don cin abinci

- Majiyar ya ce har zuwa karfe 1 na rana jami’an tsaro ba su iso yankin ba

Akalla fiye da mazauna 300 na garin Mbiabong Ito dake yankin karamar hukumar Odukpani na jihar Cross Ribas sun gudu daga gidajensu bayan da Fulani makiyaya suka mamaye yankin a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.

Rahotanni sun bayyana a ranar Laraba cewa makiyayan, wadanda suka mamaye garin da shanaye masu yawa, sun yi tsayayya ga ƙoƙarin da mazaunar garin suka yi don hana su shiga gonakin su don cin abinci.

Bayanai sun nuna cewa makiyayan sun shiga cikin garin ne daga Arochukwu, wani gari dake kudu maso gabashin jihar Abiya.

Rikicin makiyaya a jihar Cross Ribas ta tilasta wa mazaunar fiye da 300 barin gidajensu

Fulani makiyaya

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, wani dangin daya daga cikin 'yan kauyen da suka gudu, wanda ya bayyana kansa a matsayin Eyo Edet, ya ce ‘yan uwansa sun yi watsi da gidajensu kuma sun boye a cikin daji a lokacin da makiyayan suka fara harbi a iska.

KU KARANTA: Harin Borno: Maina yayi Allah wadai da harin, ya yi ta’aziya ga masarautar Biu

Edet ya ce, "Na samu kira daga ‘yan uwana na Mbiabong Ito cewa Fulani makiyaya sun mamaye garin tare da shanaye masu yawa. Ta ce fiye da mutane 300 na kauyukan suna cikin daji saboda tsoron makiyayan”.

Ya ce, "Ba za su iya komawa ba saboda har yanzu 'yan sanda ba su iso su ceto su ba har zuwa karfe 1 na rana a yau Laraba", in ji majiyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel