Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

- Ta bayar da wannan umurni ne yayin zaman tattaunawa na Kwamitin Zartarwa na Tarayya

- Kachikwu ya ce karancin man fetur din da kasa ke fuskanta ba shi da alaka da rashi

- Ya kuma tabbatar wa kwamitin cewan za su dukufa wurin magance matsalar

Gwamnatin Tarayya ta umurci karamin ministan man fetur, Dakta Ibe Kachikwu, da ya magance matsalar karancin man fetur da a ke fuskanta a fadin kasan nan, kafin karshen mako.

Ta ba shi wannan umurni ne yayin zaman tattaunawar Kwamitin Zartarwa na Tarayya da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban Kasa.

Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

Gwamnati ta umurci Kachikwu ya kawo karshen karancin man fetur kafin karshen mako

Shugaban Kasa Buhari bai samu halartar taron ba saboda ya ziyarci Jihar kano, bisa aiki. Ministan Sadarwa da Al'adu, Lai Mohammed, shi ne ya sanar da manema labarai hakan bayan kammala taron.

KU KARANTA: Coca Cola ta shawarci 'yan Najeriya su yawaita cin 'ya'yan itatuwa

Kachikwu ya tabbatar wa majalisar cewan akwai mai da zai ishe kasar har zuwa karshen Janairu na 2018. Ya ce karancin man ba shi da alaka da rashi, sai dai tsananin bukatar sa da a ke yi a lokacin sanyi.

Ya kuma ce gwamnati ba ta da burin kara kudin man fetur din sabanin yadda wadansu ke tunani. Daga karshe, ya ce za su dukufa don kawar da karancin na sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel