Nigerian news All categories All tags
Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

- Kotu ta daure Raf’iu Olagbenro bisa laifin lalata karamar yarinya a gari Ibadan

- Matasa suka kama mai laifin a lokacin da yake kan yin lalata yarinyar a cikin wani kwango

- Bincike ya nuna Rafiu yana haduwa da yarinyar ne a duk lokacin da take kan hanyar dawowa daga makaranta

Kotun majistare dake garin Ibadan a jihar Oyo ta daure wani manomi mai suna Raf’iu Olagbenro a kurkuku bisa laifin lalata wata yarinya mai shekaru goma 14.

Dansanda mai daukaka kara Ouseye Oyebanji ya fadawa kotu cewa, mai lafin Raf’iu ya saba kwanciya da wannan yarinya a unguwar su dake kauyen Abendo a duk lokacin da take kan hanyar dawowa daga makaranta.

Dansandar yace matasan unguwan ne suka kama Rafi’u a lokacin yake lalata da yarinyar a cikin wani kwango gini.

Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

Kotu ta daure wani manomi da laifin lalata yar shekara goma 14

Kakar yarinyar ta sa matasa su nemo mata jikarta bayan ta lura yarinyar bata dawo daga aiken da ta yi ma ta ba.

KU KARANTA : Trump ya bayyana niyyar sa na mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Jerusalem

Alkalin kotu Modupeola Olagbenro yaba da umarnin tsare Rafiu a kurkuku har sa kotun ta gama sauraron shawarwari daga hukumar kare hakki kanana yara a jihar.

An daga sauraro zuwa ranar 10 ga watan Janairu na sabuwar shekara 2018 dan cigaba da sauraron karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel