Ma’aikatan da gwamnatin jihar Kaduna ta sallama zasu fara karbar hakkokinsu

Ma’aikatan da gwamnatin jihar Kaduna ta sallama zasu fara karbar hakkokinsu

Gwamnatin jihar Kaduna zata fara biyan ma’aikatan kananan hukumomi da ta sallama daga bakin aiki, hakkokinsu nan da watanni biyu masu zuwa, inji rahoton Daily Trust.

Wani hadimin gwamna Malam Nasiru El-Rufai ta bangaren labaru da sadarwa, Sa’idu Adamu ya bayyana haka yayin dayake ganawa da manema labaru a ranar Talata 5 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da fitaccen jarumin Kannywood

Adamu ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin sallamar ma’aikatun ne sakamakon kananan hukumomi cunkus suke da Ma’aikata wadanda basu aikin komai, don haka gwamnatocin kananan hukumomin basa iya tabuka komai illa biyan albashi, shima sai jiha ta taimaka musu.

Ma’aikatan da gwamnatin jihar Kaduna ta sallama zasu fara karbar hakkokinsu

Ma’aikatan gwamnatin jihar Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Saidu Adamu na fadin za’a biya ma’aikatan da aka sallama albashinsu na watanni biyu, yayin da kudin fansho da na gratuti zai biyo baya cikin watanni biyu.

“An samu ma’aikata 135 masu dauke da kwalayen NCE, don haka za’a yi musu jarabawar gwaji, daga bisani a aika da duk wanda suka samu nasara makarantun Firamari don su koyar.” Inji Adamu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel