Wani ɗa- banga ya fi mai kora shafawa, ya bindige wani Magidanci a Anambra

Wani ɗa- banga ya fi mai kora shafawa, ya bindige wani Magidanci a Anambra

Idna ajali yayi kira, ko ba ciwo sai an je, wannan shine abin ya wakana tsakanin wani Magidanci mai suna Lotachukwu Nwagboso mai shekaru 34, da wani dan banga mai suna Chinedu Ibeanozie.

Shi dai Lotachukwu ya rasa ransa ne a hannun dan banga Chinedu, a yayin daya bindige shi a bisa kuskure, a garin Alaife Umuaku Uli, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Matsalolin aure: Yanzu aka fara kashe Maza – Inji wata Malama

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar Lotachukwu mai sana’ar hada wakoki ya tafi wani kauye ne don aikin hada wakoki a bikin binne wani mutumi, inda a nan ne dan bangan ya harbe shi.

Wani ɗa- banga ya fi mai kora shafawa, ya bindige wani Magidanci a Anambra

Wani ɗa- banga

Kisan mutumin ya faru ne daidai lokacin da danbangan yayi kokarin buga babur dinsa, a yayin da bakin bindigar tasa ke fuskantar mamacin.

Sai dai lamarin na faruwa, sai dan bangan ya ranta ana kare, inda har yanzu ba’a san inda ya shiga ba, amma fa matasna garin sun harzuka suka fara farfasa kadarorin dan bangan, da ma na iyalan mutumin da ake binnewa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kaakakin Yansandan jihar, Nkiruka Nwode ya ja hankalin mutane da su lura da duk danbanga wanda suke dauka aikin gadi, tare da neman goyon bayan jama’a wajen kama mutumin da ake zargi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel