Nigerian news All categories All tags
Fitacciyar 'yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin 'yan damfara

Fitacciyar 'yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin 'yan damfara

Fitacciyar 'yar gwagwarmayar nan 'yar asalin jihar Borno kuma daya daga cikin manyan jiga-jigan dake fafutukar ganin an sako 'yan matan Chibok din da aka sace Aisha Yesufu ta bayyana jam'iyyar APC mai mulki a matsayin 'yan damfara ga 'yan Najeriya.

'Yar gwagwarmayar dai tayi wannan ikirarin ne a cikin wani sako da ta aike a shafin ta na sadarwar zamani na Tuwita inda take mayar da martani ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.

Fitacciyar 'yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin 'yan damfara

Fitacciyar 'yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin 'yan damfara

KU KARANTA: Abun da Atiku ya wajaba yayi kafin ya samu tikitin takarar 2019

Legit.ng dai ta samu cewa tun farko Gwamnan na Kaduna ne a cikin wani irin salo na barkwanci ya caccaki jam'iyyar ta PDP a matsayin 'yan damfara bayan da suka ce za su yaki cin-hanci-da rashawa idan har 'yan Najeriya suka zabe su a 2019.

To sai dai wannan jawabin na Gwamnan bai yiwa 'yar gwagwarmayar dadi ba inda ta bayyana cewa ai jam'iyyar ta APC ita ce babbar damfara ga 'yan Najeriya bayan da suka sha alwashin yakar cin hanci da rashawa amma sai suka bige da kamen 'yan adawa kawai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel