Nigerian news All categories All tags
Kin zuwa Kano: Wasu mafusata sun cire katon hoton Shugaba Buhari a jihar Kano

Kin zuwa Kano: Wasu mafusata sun cire katon hoton Shugaba Buhari a jihar Kano

Yayin da siyasar manyan zabukan game-gari na shekarar 2019 ke kara karatowa, siysar na kara zafafa a wasu yankuna na kasar musamman ma jihar Kano da ke da dumbin jama'a bila'adadin kuma mabanbanta a dukkan fannonin rayuwa.

To sai dai siyasar ta jihar na so ta dauki wani sabon salo bayan da wasu mafusatan matasa a jihar suka gaggabe wani katon hoton kamfe na Shugaba Buhari da aka dasa a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin jihar ta Kano a cikin karshen makon da ya gabata.

Kin zuwa Kano: Wasu mafusata sun cire katon hoton Shugaba Buhari a jihar Kano

Kin zuwa Kano: Wasu mafusata sun cire katon hoton Shugaba Buhari a jihar Kano

KU KARANTA: Kishi ko hauka: Wata mata ta kashe dan kishiyar ta da gubar bera

Legit.ng dai ta samu cewa mafusatan matasan dai sun yi maganganu marasa dadi ga shugaban yayin da suke kokarin gaggabe hoton musamman ma dai yadda shugaban ya ki zuwa jihar ta su tun bayan darewar sa karagar mulki tare da taimakon miliyoyin ruwan kuri'un da suka yi masa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a karo da dam dai shugaban na sanyan rana da lokacin zuwa jihar amma sai ya fasa, lamarin da ko kusa baya yi wa 'yan jihar dadi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel